ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Wafa na falasdinawa ya bada rahoton cewa yahudawan sun farwa falasdinawa masu zanga zanga a yankin yamma da kogin Jordan wadanda suka hada da garin Nablus, Biitaa da kuma Jabal-Sabih, inda suka jiwa falasdinawa da dama rasuna. Daga cikinsu akwai mutane 146 a garin Nablusn.
Ahmad Jibril shugaban hukumar hilal Ahmar ko red cross a yankin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa an harbi mutane 33 da harsasai na gaskiya sannan wasu 87 saboda shakar hayaki mai sa hawaye sun shake.
342/